Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tuni likitoci suka fara duba lafiyar yaron, mai kimanin shakara 5, kuma rahotanni daga kasar sun ce yaron ya samu karaya da dama.
Yaron, ya fada cikin rijiyar ne mai zurfin mita 32 a ranar Talata inda rahotanni suka ce ya fada ne a lokacin da yake wasa a kusa da rijiyar.
Batun Rayon dai ya dau hankali a kasar dama duniya musamman a kafafen sada zumunta, inda ake ta yi masa addu’o’i.
342/